A ran 6 ga wata da dare, James Soong, shugaban jam'iyyar PFP ta Taiwan ya shugabanci kungiyar jam'iyyar ta kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ta isa birnin Nanjing, wannan ya zama zango na 2 ne da ya ya da cikin ziyarar da ya yi a babban yankin kasar Sin.
An ce, a lokacin kungiyar yin ziyara take birnin Nanjing, za ta kai ziyarar ban girma ga kabarin Mr. Sun Yat-sen, madugun juyin juya halin demokuradiya na kasar Sin, wato kabarin Yat-sen na birnin Nanjing.
Jemes Soong ya kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ne daga ran 5 ga wata bisa gayyatar da kwamitin tsakiya na J.K.S. da Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya yi masa. Kafin ya isa birnin Nanjing kuma James Soong da 'yan rakiyarsa sun yi ziyara a birnin Xi'an. (Umaru)
|