Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-06 17:13:39    
Sinawa 'yan kaka-gida sun yaba wa ziyarar da Lien Chan, shugaban KMT ya yi a nan babban yankin kasar Sin

cri
A cikin 'yan kwanakin nan, kungiyoyi da kafofin watsa labaru na Sinawa 'yan kaka-gida wadanda suke da zama a kasar Australiya da Romania da Argentina bi da bi ne suka bayar da sanarwoyi da bayanai, inda suka yaba wa ziyarar da Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya yi a nan babban yankin kasar Sin da shawarwari mai ma'anar tarihi da aka yi a tsakanin shugabannin jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

A ran 4 ga wata, kungiyar Australiya ta sa kaimi ga dinkuwar duk kasar Sin ta bayar da wata sanarwa, inda aka ce, ziyarar da Lien Chan ya yi a babban yankin kasar Sin da shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin suka yi musafaha da juna bayan shekaru 60 da suka wuce, muhimman al'amura ne da za a rubuta su a cikin tarihin bunkasuwar kabilun kasar Sin. (Sanusi Chen)