A ran 5 ga wata, James Soong, shugaban jam'iyyar the People First Party ya shugabanci kungiyar kawo wa babban yankin ziyara ta jam'iyyar ya fara yin ziyara a nan babban yankin kasar Sin. Kafofin Taiwan da Hongkong da Macao sun mai da hankali sosai kan ziyarar.
A ran 5 ga wata, jaridar Lian He da jaridar Zhongyang Daily da jaridar China Times na yankin Taiwan da wasu gidajen rediyo mai hoto sun bayar da labari game da ziyarar da James Soong ya fara yi a babban yankin kasar Sin a kan muhimmin shafin jaridunsu ko a cikin lokaci. Jaridar Lian He ta kuma bayar da wani bayanin edita cewa, ziyarar da James Soong ke yi a babban yankin kasar Sin ta isa a jira shi.
A wannan rana, jaridar Wen Hui ta Hongkong ta kuma bayar da wani bayanin edita, cewa ana cike da imani cewa ziyarar da James Soong ke yi za ta kara kafa kyawawan sharuda kan yadda za a nemi ra'ayi daya kuma za a kawar da bambanci, kuma za a nemi bunkasuwa cikin lumana har za a samu bunkasuwa tare a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.
Bugu da kari kuma, jaridar Macao Daily ta bayar da wani bayanin edita, cewa ziyarar da James Soong ke yi a babban yankin kasar Sin za ta ba da gudummawa sosai wajen ciyar da dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan gaba. (Sanusi Chen)
|