Ran 4 da dare, kotun musamman na MDD da ke kasasr Saliyo ya bayar da wata sanarwa a kan shafin internet nasa, inda aka bukaci kasar Nijeriya da ta mika wa kotun Charles Taylor, tsohon shugaban kasar Liberia, wanda ke gudun hijira a kasar Nijeriya.
Cikin sanarwar, an ce, Mista Taylor yana da allaka da kungiyar al-Qaeda, kuma yana yunkurin ta da hargitsi a yammacin Afirka, bai kamata ba kasar Nijeriya ta ci gaba da bayar masa taimako. Har wa yau kuma, kotun musamman ya yi kira ga shugaba Bush na kasar Amurka da shugaba Obasanjo na kasar Nijeriya da su sake yin la'akari kan batun mika Mista Taylor ga kotun, a yayin da suke ganawa a birnin Washington a ran 5 ga wata. (Bello)
|