A ran 6 ga wata, shugaba James Soong na jam'iyyar the People First Party ya shugabanci kungiyar kawo wa babban yanki ziyara ta jam'iyyar da su je kabarin kakannin-kakannin farko na kabilun kasar Sin da ke lardin Shaan'xi, inda suka yi gagarumin biki domin nuna mubaya'ar ban girma ga Huangdi, kakannin-kakannin farko na kabilu daban-daban na kasar Sin.
A wannan rana da safe, bayan an kawo karshen bikin nuna mubaya'ar ban girma ga kabarin Huangdi, Mr. James Soong ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, Huangdi kakannin-kakannin daya ne ga dukkan kabilun kasar Sin. 'Yan uwanmu da ke zama a gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan muna da kakannin-kakanni daya, kuma al'adun kabilun kasar Sin suna da asali daya. Mr. James Soong yana fatan Sinawan da ke da zama a gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan za su kaunar juna kuma kawo alheri ga dukkan Sinawa. (Sanusi Chen)
|