
James Soong, shugaban jam'iyyar People First Party zai fara ziyararsa a babban yankin kasar Sin a ran 5 ga wata. A yau Laraba, Mista Soong ya kira taron maneman labaru a birnin Taipei, inda ya nuna fatansa cewa ziyararsa za ta sa kaimi ha hadin kan Sinawa da ke gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.
Mista Soong ya ce, zai tsaya kan manufar kasar Sin daya tak, da ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992, da kuma matsayinsa na ki amince da 'yancin kan Taiwan. Yana fata ziyarar da zai yi za ta ba da taimako wajen samun kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, kuma zai iya cimma daidaito tare da bagaren babban yankin kasar Sin. (Bello)
|