
A ran 4 ga wata, kafofin watsa labaru na Taiwan bi da bi ne suka bayar da labari game da sauye-sauyen da ziyarar da Lien Chan ya yi a babban yankin kasar Sin ta kai wa Taiwan, inda suka bayyana cewa, tare da nasara ne ziyarar Lien Chan ta sake halin da ake ciki a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma ta bayyana ra'ayin yawancin jama'ar Taiwan na neman zaman lafiya a tsakanin gabobin 2.
Jaridar China Times ta Taiwan ta bayar da wani bayanin edita cewa, halin da ake ciki yanzu a tsakanin gabobin 2 da yawancin jama'ar Taiwan suke nema ba halin adawa da juna a tsakanin gabobin 2 ba, amma halin kiyaye zaman lafiya da yin mu'ammala da juna da ake ciki a tsakanin gabobin 2. (Sanusi Chen)
|