Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-04 17:49:16    
Kafofin watsa labaru na Hongkong sun yaba wa sahihin da babban yankin kasar Sin ya bayyana wajen dangantakar da ke tsakanin gabobin 2

cri
A ran 4 ga wata bi da bi ne kafofin watsa labaru na Hongkong suka bayar da bayanan edita, inda suka nuna cewa, a shekaranjiya, samar wa Taiwan panda guda 2 da sauran matakai guda 2 da babban yankin kasar Sin ya shelanta suna cike da sahihanci da kirki. Wannan sahihanci ya samar da babbar dama ga ayyukan shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa mai dorewa a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Bayanan edita suna fatan hukumar Taiwan za ta bi ra'ayoyin jama'a kuma za ta bi wata sabuwar hanya wajen daidaita dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu.

Kafin Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya kawo karshen ziyararsa a nan babban yankin kasar Sin ne, bangaren babban yankin kasar Sin ya shelanta wadannan matakai 3 da zai dauka. Sauran matakai 2 su ne, bangaren babban yankin kasar Sin zai bai wa mazaunan babban yankin izinin yin yawon shakatawa a taiwan da za a kara shigowa da 'ya'yan itatuwa na Taiwan zuwa nan babban yankin. (Sanusi Chen)