Shugaban jam'iyyar People First Party Mr. James Soong zai shugabanci wata kungiya domin kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara daga gobe wato ran 5 ga watan nan. ya zuwa yanzu, bangaren babban yankin kasar Sin ya riga ya shara fage domin maraba da James Soong da 'yan rakiyarsa.
James Soong da 'yan rakiyarsa za su kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ne bisa gayyatar da tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma Hu Jintao, babban daraktan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin suka yi musu, kuma za su yi ziyara a biranen Xi'an da Nanjing da Shanghai da Changsha da kuma Beijing. Yayin da suke cikin birnin Beijing, Hu Jintao da sauran shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za su yi ganawa da kungiyar ziyara, da kuma yi shawarwari tare da James Soong.(Kande Gao)
|