Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-04 16:56:52    
Kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun yaba wa ziyarar da Lien Chan ya yi a nan babban yankin kasar Sin

cri
A 'yan kwanakin nan, kafofin watsa labaru na Faransa da Syria da Venezuela sun bayar da bayanai, inda suka yaba wa ziyarar da Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya yi a nan babban yankin kasar Sin da shawarwarin da aka yi a tsakanin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin.

A ran 3 ga wata, jaridar Europe Times ta kasar Faransa ta buga wani bayanin edita, inda aka bayyana cewa, babban sakamkon da Lien Chan ya samu a gun wannan ziyara shi ne an sake yin musanye-musanye da yin shawarwari kan dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan wadda ta shiga uku a sakamakon yunkurin neman 'yancin kan Taiwan da aka yi a Taiwan.

A wannan rana kuma, jaridar Tishirin ta gwamnatin kasar Syria ta buga wani bayani, inda aka fadi cewa, ziyarar da Lien Chan ya yi a babban yankin kasar Sin da shawarwarin da aka yi a tsakaninsa da Hu Jintao, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin babban cigaba ne da aka samu wajen kawar da nukurar da aka yi a tsakanin jam'iyyun nan biyu har shekaru 60 da suka wuce. (Sanusi Chen)