
A ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin shugaban ofishi mai kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato CPC, Mr. Wang Zaixi ya bayyana a gun wani taron manema labaru, cewa ziyarar da Mr. Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya yi a nan babban yankin kasar Sin ta ci nasara kwarai.
Mr. Wang Zaixi ya ce, ziyarar da Mr. Lien Chan da kungiyar kawo wa babban yankin ziyara ta jam'iyyar KMT ta kasar Sin suka yi a nan babban yankin, wani muhummin al'amari ne a cikin tarihin dangantakar da ke tsakanin jam'iyyar CPC da jam'iyyar KMT, ita kuma wani muhimmin al'amari ne ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Ganawa da shawarwarin da aka yi a tsakanin Hu Jintao da Lien Chan sun zama shawarwari mai ma'anar tarihi da aka yi a tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar CPC da jam'iyyar KMT a cikin shekaru 60 da suka wuce. Tabbas ne irin wannan shawarwari zai ba da amfani sosai kan yadda za a ingiza bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobin 2. (Sanusi Chen)
|