Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-03 16:25:23    
Lien Chan ya koma Taiwan

cri
A ran 3 ga wata, Mr. Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin wanda ya shugabanci wata kungiyar kawo wa babban yankin ziyara ta jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin, ya gama ziyararsa ta kwanaki 8 a nan babban yankin kasar Sin kuma ya tashi daga birnin Shanghai zuwa Hongkong domin koma birnin Taibei na lardin Taiwan.

Bisa gayyatar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin,wato CPC da babban sakataren jam'iyyar CPC Mr. Hu Jintao suka yi masa ne, Lien Chan da 'yan rakiyarsa suka kawo wa babban yankin ziyara. A lokacin da suke yin ziyara a nan babban yankin, Hu Jintao da Lien Chan sun yi shawarwari kuma sun bayar da sanarwar yada labaru, inda aka ce, jam'iyyun nan biyu za su ingiza gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da su komar da yin shawarwari na zaman daidai wa daida tun da wuri bisa ka'idar Sin daya tak da suka amince tare a shekarar 1992. Ban da wannan, jam'iyyun nan biyu za su ingiza da a kawo karshen halin adawa da juna a tsakanin gabobin 2, kuma za su ingiza da a kara yin mu'ammalar tattalin arziki daga duk fannoni a tsakanin gabobin nan biyu. Sabo da haka, ana ganin cewa, ba ma kawai ziyarar da Lien Chan ya yi ta bude sabon shafi ga dangantakar da ke tsakanin jam'iyyar CPC da jam'iyyar KMT a cikin tarihi ba, har ma tabbas ne za ta yi tasiri sosai kan yadda za a ingiza da bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu.

A ran 26 ga watan Afrilu ne, kungiyar kawo wa babban yankin ziyara ta jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ta iso nan babban yankin. A cikin kwanaki 8 da suka wuce, daya bayan daya ne Lien Chan da 'yan rakiyarsa suka ziyarci birane 4, wato Nanjing da Beijing da Xi'an da kuma Shanghai. Wannan kuma karo na farko ne da shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya kawo wa babban yankin ziyara a cikin shekaru 56 da suka wuce, bayan jam'iyyar ta je tsibirin Taiwan a shekarar 1949 domin ta ci hasara a cikin yakin basasa na kasar Sin. (Sanusi Chen)