
Kwanakin baya kafofin watsa labaru na kasar Singapore da Thailand da Indonesia da Bulgria sun yi ta bayar bayanoni don buga take ga ganawa mai ma'anar tarihi da aka yi a tsakanin Hu Jintao, babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin.
A ran 2 ga watan nan jaridar Hadaddiyar jaridar safe ta kasar Singapore ta bayar da ra'ayin edita cewa, Hu Jintao da Lien Chan sun yi ganawa mai ma'anar tarihi, inda suka nuna burin tarayya na kiyaye zaman lafiya da sa kaimi ga aikin raya kasa.
Jaridar The Monitor da a ke bugawa a kasar Bulgaria ta bayar da sharhi cewa, ganawar da aka yi a tsakanin Hu Jintao da Lien Chan ta shaida cewa, jam'iyyun nan biyu suna son soke nukurar da ke tsakaninsu da yin sulhu, wanann yana da muhimmancin gaske ga jama'ar gabobi biyu har ma ga duk duniya. (Dogonyaro)
|