Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-02 16:45:27    
Sakataren kwamitin birnin Shanghai na JKS ya gana da Lien Chan

cri

A ran 1 ga wata da maraice, Mr. Chen Liangyu, sakataren kwamitin birnin Shanghai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gana da Mr. Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da sauran membobin kungiyar kawo wa babban yankin ziyara ta KMT. Mr. Chen Liangyu ya kuma shirya su liyafa.

A gun ganawar, Chen Liangyu ya ce, tabbas ne ziyarar da Lien Chan ke yi a nan babban yankin za ta kara ingiza yin hadin guiwa da musanye-musanye a tsakanin gabobin biyu.

Mr. Lien Chan ya ce, dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan matsala ce da ke jawo hankulan duk duniya. Jam'iyyarsa ta kan yi kokari kan yadda za a ingiza gabobin biyu da su kafa dangantakar moriyar juna da taimaka wa juna da kuma samun nasara tare. Mr. Lien ya kara da cewa, da gabobin biyu su fuskanta halin da ake ciki yanzu kuma na nan gaba, tabbas ne za su iya kafa zaman lafiya a tsakaninsu, kuma za su iya samun bunkasuwa tare. (Sanusi Chen)