Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-02 16:33:45    
Wang Daohan ya gana da Lien Chan

cri
A ran 2 ga wata da safe a birnin Shanghai, Mr. Wang Daohan, shugaban kungiyar kula da dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan ta kasar Sin ya gana da Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da 'yan rakiyarsa wadanda suke ziyara a birnin Shanghai.

A gun ganawar, Wang Daohan ya ce, cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, muna fatan alheri ga kyautatuwa da bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma muna kokari kan yadda za a kara yin mu'ammala da cudanya a tsakanin jama'ar gabobin biyu kuma za a kyautata dangantakar siyasa a tsakanin gabobin biyu.

Bugu da kari kuma, Wang Daohan ya bayyana cewa, muna fata za mu gama kan dukkan jam'iyyun siyasa da kungiyoyi iri iri da jama'a wadanda suke amincewa da ra'ayin Sin daya tak da aka samu a shekarar 1992, kuma suke fama da yunkurin neman 'yancin kan Taiwan domin bayar da kokari tare kan yadda za a ingiza raya dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 cikin lumana kuma cikin hali mai dorewa. (Sanusi Chen)