
A ran 1 ga watan Mayu da yamma, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin Lien Chan da kungiyar kawo babban yankin kasar Sin ziyara ta jam'iyyar KMT wadda ke karkashin jagorancinsa sun isa birnin Shanghai domin ci gaba da ziyararsa a babban yankin kasar Sin.
Birnin Shanghai wurin karshe ne da kungiyar ta yada zango a cikin wannan ziyara. A birnin Shanghai, Mr. Lien Chan zai gana da shugaban kungiya mai kula da dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan Mr. Wang Daohan. Ban da wannan, Mr. Lien zai gana da 'yan kasuwa na Taiwan wadanda suke aiki a birnin Shanghai. (Sanusi Chen)
|