Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-29 21:44:33    
Hu Jintao ya yi shawarwari da Lien Chan kuma ya gabatar da ra'ayoyi 4 kan dangantakar da ke tsakanin gabobi 2

cri

A ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ya yi shawarwari da Lien Chan, shugaban jam'iyyar KMT ta kasar Sin wanda ke shugabantar kungiyar yin ziyara a babban yankin kasar. Wannan shawarwari ya zama karo na farko ke nan da ake yi tsakanin muhimman shugabannin jam'iyyun 2 tun bayan shekaru 60 da suka wuce. A gun shawarwarin, Hu Jintao ya gabatar da ra'ayoyi 4 wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobin 2.

Wadannan ra'ayoyi 4 da Hu Jintao ya gabatar su ne, na farko, a amince wa juna wajen siyasa, da girmama wa juna, da neman ra'ayi daya a kan manyan abubuwa masu muhimmanci kuma a kawar da bambanci a kan kananan abubuwa marasa muhimmanci, da tabbatar da samun bunkasuwar dangantaka tsakanin gabobin 2 cikin zaman lafiya da dorewa. Na 2, kara karfin musanye-musanye da hadin gwiwa wajen tattalin arziki, da samun moriyar juna da samun bunkasuwa tare. Na 3, yin shawarwari cikin daidaici da kara samun ra'ayi daya daga sauran fannoni. Na 4, himmantar da jama'ar gabobin 2 da su kara yin mu'amalar juna da kara fahimtar juna.

Bugu da kari kuma, Hu Jintao ya bayyana cewa, 'yan uwanmu na gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan masu jini daya ne. 'Yan uwa na babban yanki muna fahimta kuma muna girmama zuciyar kishin kasa ta 'yan uwanmu na Taiwan sosai. Muna kuma gafarta duk wata gurguwar fahimtar da 'yan uwanmu na Taiwan suka yi wa babban yankin a cikin tarihin musamman domin dalilai iri daban-dabam.

Mr. Lien Chan ya bayyana cewa, jam'iyyar Kuomintang yana fama da yunkurin neman 'yancin kan Taiwan, kuma tana fata gabobin biyu za su yi mu'ammala a tsakaninsu bisa ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992. Sa'an nan kuma za a iya kafa sharadin raya dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 cikin lumana, har za a iya ingiza gabobin biyu da su kai ga daddale wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a tsakaninsu. (Sanusi Chen, Umaru)