A ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS da Lien Chan, shugaban Jam'iyyar KMT ta kasar Sin sun yi shawarwari na karo na farko tun shekaru 60 da suka wuce a tsakanin muhimman shugannin jam'iyyun 2, sun sami ra'ayi daya na tsayawa kan ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992 wanda ya bayyana ka'idar kasar Sin daya a duniya, da yin adawa da rukunin 'yan kawo baraka na Taiwan.
Cikin sanarwar da aka bayar bayan shawarwarin an ce, jam'iyyun 2 sun tsaya kan ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992 da yin adawa da rukunin 'yan kawo baraka na Taiwan, neman zaman lafiya da dorewa na shiyyar mashigin tekun Taiwan, da sa kaimi ga bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobin 2, da kiyaye moriyar tarayya ta 'yanuwa na gabobin 2 sun zama ra'ayi daya na jam'iyyun 2. Jam'iyyun 2 kuma za su sa kaimi ga sake yin shawarwari tsakanin gabobin 2 tun da wuri bisa harsashin ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992. Ban da wannan kuma jam'iyyun 2 sun tsai da kudurin kafa dandalin yin mu'amalar juna tsakaninsu bisa kayadadden lokaci. (Umaru)
|