Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-29 18:27:26    
Shugabannin CPC da KMT sun gana da juna

cri

A ran 29 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, Hu Jintao babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato CPC da shugaba Lien Chan na jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin(KMT) wanda ke yin ziyara a nan babban yankin kasar Sin sun yi shawarwari, inda suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan wasu muhimman maganganu ciki har da yadda za a kyautata da raya dangantaka a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da cudanyar a tsakanin jam'iyyar KMT da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Wannan ne karo na farko da shugabannin jam'iyyun nan biyu suka yi shawarwari a cikin shekaru 60 da suka wuce.

Kafin su yi shawarwari, Hu Jintao ya yaba wa ziyarar da Lien Chan ke yi a nan babban yanki. Hu Jintao ya ce, ba ma kawai wannan wani muhimmin al'amari ne a cikin tarihin dangantakar da ke tsakanin jam'iyyun biyu ba, har ma shi ne wani muhimmin al'amari ga dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu. Mr. Hu ya jadadda cewa, a yayin da gabobin biyu suke cikin mawuyacin hali, ya kamata jam'iyyun nan biyu su yi kokari kan yadda za su bayyana wa 'yan uwanmu na gabobin biyu hangen nesa na dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu da na samun bunkasuwa mai dorewa cikin lumana. Ban da wannan. Ya kamata su bayyana wa duk duniya karfi da basira na dukkan Sinawa na gabobin biyu yadda suke kawar da bambanci da matsalolin da suke kasancewa a tsakanin gabobin biyu yanzu. Bugu da kari kuma, Mr. Hu ya ce, ya kamata gabobin biyu su nemi makomar zaman lafiya da ta karko ga dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu domin cimma burin bunkasa duk kasar Sin gaba daya.

Mr. Lien Chan ya ce, ya kamata hukumomin gabobin biyu su mai da hankali kan moriyar duk kasar Sin bisa tushen amincewa da juna. (Sanusi Chen)