Ran 29 ga wata yayin da shugaba Lien Chan na jam'iyyar Kuomintang na Sin da ya shugabanci wata tawagar ziyarci babban yankin kasar Sin, ya yi jawabi a jami'ar Beijing, shaharariyar jami'ar kasar Sin, ya nuna cewa, kamata ya yi gabobin biyu su tsaya kan shinfida zaman lafiya da dosa wa samun nasara tare.
Lien Chan ya ce, yunkurin tarihi da ra'ayoyin jama'a sun sa ya kara karfin zuciya wajen gabatar da ra'ayin nan. A mai da mutane a gaban kome, samun zaman alheri ya sama wani abu na farko, sun zama nufin da jama'ar gabobi biyu ke nuna goyon bayan tare , jama'ar ba sa son gani yin nukura da juna tsakanin gabobin biyu, suna son gani yin tattaunawa da samun jituwa da hadin kai.
Lien Chan ya tsaya a kan cewa, a gaban halin da ke ciki a gabobin biyu, dole ne gabobin biyu su kare zama mai dorewa da neman ra'ayi daya kan banbance-banbance, tattara kyakkyawar niyya don bude wani sabuwar makoma.(ASB)
|