Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-29 11:45:09    
Majalisar rikon kwarya ta kasar Iraki ta zartas da sunayen wadanda za su shiga sabuwar gwamnati

cri

A ran 28 ga wannan wata, majalisar rikon kwarya ta kasar Iraki ta zartas da sunayen mambobin gwamnatin rikon kwarya wadanda firayim ministan wucin gadi na kasar Ibrahim Al-Jarafi ya gabatar bisa kuri'u masu rinyaje, bayan watanni uku da aka kammala babban zabe a karshen watan Janairu na shekarar da muke ciki, a karshe dai kasar Iraki ta kafa sabuwar gwamnatinta.

Mun sami labari cewa, mutane 185 da ke cikin 'yan majalisar rikon kwarya ta kasar Iraki sun halarci taron da aka yi a wannan rana, daga cikinsu mutane 180 sun jafa kuri'un nuna amincewa don nuna goyon baya ga sunayen mambobin majalisar ministoci da Mr Jafari ya gabatar. Sabuwar majalisar ministoci ta kafa kujeru 36, wato mukamai 36 ke nan, tana kunshe da mataimakan firayim ministan kasar guda 4 tare da ministoci 32, ciki har da mata guda 7.

Bayan da majalisar rikon kwarya ta zartas da sunayen mambobin majalisar ministoci, Mr Jafari ya bayar da jawabi, inda ya bayyana cewa, rukunonin siyasa daban daban na kasar Iraki dukansu suna da ikon shiga cikin gudanarwar siyasa ta nan gaba ko su shiga sabuwar gwamnati ko a'a.

Zartas da sunayen nan ya alamanta cewa, gwamnatin farko da jama'a ke zaba a cikin shekaru fiye da 50 ta kafu, kuma ya kawo karshen halin kaka-ni-ka-yi da rukunoni daban daban na kasar Iraki suke ciki har tsawon wasu watanni wajen daidaita batun kafa sabuwar gwamnati , wannan ya bayyana cewa, kasar Iraki ta sami ci gaba mai muhimmanci wajen farfado da harkokin siyasa , kuma zai ba da taimako ga mayar da kwanciyar hankali da zaman karko a kasar Iraki.

Babbar dawainiyar da ke gaban Mr Jafari da sabuwar gwamxnati ita ce daukar nauyi bisa wuyansu don tsara wani tsarin mulkin kasa da kuma raba gardamar jama'a a kan wannan tsarin mulkin kasar . Dayake sabuwar gwamnati ta Jafari ta sami cikas a fannoni da yawa , shi ya sa za ta gamu da matsaloli da kalubale da yawa a nan gaba.

Da farko, sunayen da Mr Jafari ya gabatar ba su zama cikakku ba, kuma ba a kawo karshen shawarwari kan kafa majalisar ministoci ba, aikin karshe na kafa sabuwar gwamnati yana kuma fuskatar matsaloli da yawa.

Na biyu, ana ganin cewa, Mr Jafari da kawancen hadin kai suna da sharadin bin wani addini da nuna goyon baya ga kasar Iran, a lokacin da za su aiwartar da harkokin mulki a nan gaba, za su iya gamuwa da katangogi iri iri da kasar Amurka za ta kafa musu.

Na uku, Har zuwa yanzu ba a ganin alamar samun kyautatuwa a kan muhallin tsaron kai a kasar ba.

Na hudu, bayan babban zaben da aka yi a kasar Iraki, matsayin siyasa na rukunin darikar Sunni da na darikar Shi'te da na mutanen Kurd sun riga sun sami manyan sauye-sauye, a kai a kai ne aka gefantar da rukunin Sunni daga wajen harkokin siyasa bisa sanadiyar rashin masu jefa kuri'a da yawa, rukunin darikar Shi'ate da mutane Kurd suna kasancewa cikin sabani sosai bisa sanadiyar raba fa'ida ba bisa daidaici ba a tsakanin kabilu daban daban da addinai daban daban, saboda haka siyasar kasar Iraki tana shiga halin kaka-ni-ka-yi na tsawon watanni uku bayan babban zabe. Kafofin dillancin labaru na kasashen Larbawa suna ganin cewa, kafa majalisar ministoci ba gwagwarmar karshe da bangarorin uku suke yi ba, gudanarwar harkokin siyasa ta nan gaba za ta iya shiga mawuyacin hali bisa sanadiyar sabanin da ke tsakanin bangarorin uku.

Kodayake hakan aka samu, amma,kafuwar sabuwar gwamnati a kasar Iraki ita ma ta sami karbuwa daga cikin kasar Iraki da gamayyar kasa da kasa. A cikin kasar Iraki, ana fatan sabuwar gwamnati za ta aiwatar da hakkinta tun da wurwuri da kuma gaggauta ci gaban gudanarwar harkokin siyasa a kasar da kuma dosawa gaba bisa hanyar da ake bi don mayar mutanen Iraki don su da kansu su aiwatar da harkokinsu.(Halima)