
Shugaban jam'iyyar Kuomintang (KMT) Lien Chan ya ba da lacca a shahararriyar Jami'ar Beijing a yau ran 29 ga watan nan da safe. Wannan muhimmin aiki ne da Mr. Lien Chan ya yi a gun ziyararsa ta kwanaki 8 a babban yankin kasar Sin.
Bisa ajandar da aka yi, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao za gana da Mr. Lien Chan da 'yan rakiyarsa a ran nan da yamma, inda za su yi musayar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 da kuma yin cudanya a fannonin tattalin arziki da ciniki da kuma al'adu, a lokacin nan shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar Kuomintang za su yi musafaha a karo na farko bayan shekaru 60 da suka wuce.(Tasallah)
|