Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-28 21:15:14    
Jia Qinglin ya gana da Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da kungiyarsa

cri

A ran 28 ga watan nan Jia Qinglin, manban zaunannen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gana da kungiyar kawo ziyara a babban yanki ta jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin da ke a ragamar shugaba Lien Chan, inda ya yi wa jam'iyyar Kwamintan babban yabo sabo da ta amince da ra'ayi daya na shekara ta 1992, tana yin adawa da "'yancin kan Taiwan", tana sa kaimi ga dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu, kuma tana yin kokarin neman zaman lafiya da dorewa na shiyyar Taiwan.

Jia qinglin ya nuna cewa, ziyarar da shugaba Lian Zhan ke yi wata muhimmiyar cudanya da tattaunawa ce a tsakanin jam'iyyar Kuomintang da jam'iyyar kwaminis.

Lien Chan ya ce, wannan ziyarar da ya kawo a babban yanki gudanawa ce ta tarihi, kuma goyon baya ne na bainal jama'ar Taiwan, yana fatan za a kawo wa dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu makoma mai kyau. (Dogonyaro)