Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar a ran 27 ga wata, an ce, ziyarar da Mr. Lien Chan, shugaban jam'iyyar Kuomingtang ta kasar Sin, ke yi a nan babban yankin kasar Sin ta jawo hankulan jama'ar Taiwan sosai. Wasu mutanen Taiwan sun ce, wannan ziyara za ta ba da taimako ga kara yin mu'ammala a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma zai sassauta hali mai tsanani har zai tabbatar da zaman karko a tsakaninsu. Sabo da haka, wannan ziyara abu ne da ya isa a yaba shi.
Ban da wannan, a ran 27 ga wata, lokacin da kafofin watsa labaru na Taiwan suke sharhi kan ziyarar da Lien Chan ke yi a nan babban yankin, sun bayyana cewa, dama irin ta tarihi ta riga ta iso a gabanmu, ya kamata karamin takin da Lien Chan ke yi ya zama babban taki wajen raya dangantakar da ke kasancewa a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. (Sanusi Chen)
|