Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-27 11:02:13    
Al Jafari ya gabatar da jerin sunayen ministoci ga kwamitin shugaban kasa na Iraq

cri
A ran 26 ga wata, Kakakin Ibrahim Al-Jafari da aka gabatar da shi a matsayin firayim ministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Iraq ya tabbata da cewa Al-Jafari ya riga ya tsara wani jerin sunayen 'yan majalisar ministoci,kuma ya mika shi ga shugaban kasa Jalal Talabani.Idan jerin sunayen nan ya samu amincewa daga kwamitin shugaban kasa wanda ya kunshe da Jalal Talabani da mataimakansa guda biyu su Adil Abd Al-Mahdi da Ghazi Al-Yawar,sa'an nan Al-Jafari zai gabatar da jerin sunayen ga majalisar dokoki ta rikon kwarya domin duddubawa.

A ran 26 ga wata Jawad Al-Maliky,mutum na biyu mafi girma cikin jam'iyyar the Islamic Dawa Party dake karkashin jagorancin Al-Jafari ya fayyace cewa da akwai kujerun ministoci 33 a cikin sabuwar majalisar.Daga cikinsu kawancen hadin kai wanda ya fi girma cikin jam'iyyun siyasa a majalisar dokoki ta Iraq ta samu kujeru 17,kawancen Kurdawa a matsayi na biyu a cikin majalisar dokoki ta samu kujeru 8,jam'iyyar Sunni wadda ke wakiltar musulmi sunni da suka dau kashi 20 cikin kashi dari na yawan mutanen Iraq ta samu kujeru shida.Ban da wannan kuma jam'iyyar Turkoman da kungiyar Katolika kowacensu ta sami kujera daya.Bisa labarin da wani mutum dake cikin kawancen hadin kai ya bayar,an ce da akwai matamakan firayim minista guda uku a cikin sabuwar gwamnati,kawancen hadin kai da kawancen Kurdawa da kuma mabiyar addinin sunni kowacensu ta sami kujera daya.Kawancen siyasaa wanda firayim ministan gwamnatin rikon kwarya dake da kujeru 40 a cikin majalisar dokoki bai samu kujera ko daya a cikin majalisar ministoci ba.

Kafofin yada labarau ba Larabawa sun bayyana cewa jerin sunayen 'yan majalisar ministoci da Al-Jafari ya gabatar ya yi nuni da cewa shirye-shiryen sabuwar gwamnati ya tabbatu,zai kawo makoma mai haske ga sa aya ga halin-kaka-nika yi wajen siyasa da aka samu cikin 'yan makonni saboda gwagwarmayar da aka yi domin neman kujerun ministoci a cikin sabuwar majalisar da taka rawar gani mai amfani wajen kwantar da halin siyasa da kuma sa aya ga tarzoma da kasar Iraq ke ciki a halin yanzu.Idan jerin sunayen nan zai samu amincewa daga kwamitin shugaban kasa,haka kuma zai iya samun amincewa daga majalisar dokoki ta haka kuwa majalisar dokoki zai iya amince da jerin sunanyen da firayim ministan zai gabatar ta hanyar kada kuri'a.

Wasu masu binciken al'amuran yau da kullum na nuna cewa Al Jafari ya gabatar da wannan jerin sunayen ministoci ne cikin matsin lamba na gida da na waje.Daga wani hannu saboda aka gaza kafa sabuwar gwamnati cikin lokaci cikin lokaci,harkokin tsaro na cigaba da tabarbarewa,mutanen Iraq da suka sha wahalar hare hare cikin dogon lokaci suna so a kafa sabuwar gwamnati cikin sauri domin mayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gida.A wani hannu daban kuwa Amurka ta sha matsa wa shugabannin Iraq lamba da su gaggauta kafa majalisar ministoci domin moriyarta.Kwanakin baya mataimakin shugaban kasar Amurka Cheyney da sakataren harkokin waje Condoleezza Rice sun bukaci kawancen hadin kai da kawancen Kurdawa da su hada kansu da gaggauta kafa sabuwar gwamnati.Sabo da haka a ganin masu binciken al'amuran yau da kullum da wuyan jerin sunayen ministocin da Al-Jafari ya gabatar ya samu goyon baya mai rinjaye domin ya tsara shi ne cikin gaggauwa.

A ran 26 ga wata 'yan majalisar dokoki guda uku masu bin darikar sunni daga cikin kawancen hadin kai su Fawaz Al-Jarba da Mudhar Shawkat da Abd Al-Rahman al-Niaimi sun bayyana cewa sun janye jikinsu daga kawancen hadin domin nuna kiyewa ga kawancen hadin kai saboda ya gefentar da Larabawaa masu bin darikar sunni,a sa'i daya sun bayyana matsayinsu na yin adawa da kungiyoyin kasashen waje da su yi katsalanda cikin harkokin kafa majalisar ministoci.A ran 26 ga wata gidan telebiji na Al-Jazeera ya tsamo wani labari daga majiyar labarai na kasar Iraq cewa jam'iyyar sunni dake karkashin jagorar mataimakin shugaban kasa Ghazi Al-Yawar kujerar minista ta bakwai?ministan ilmi,shawarwari tsakanin bangarori biyu kan kafa majalisar ministoci bai kare ba.Wani mutum daga cikin kawancen hadin kai ya tabbata da cewa Al-Jafari yana nan yana jiran jerin sunayen ministoci da 'yan sunni za su gabatar,idan ya samu zai iya mika cikakken jerin sunayen majalisar ministoci ga majalisar dokoki.

Ban da wannan,an kawar da rukunin Iyad Allawi,kawancen siyasa mafi girma a cikin majalisar dokoki daga majalisar ministoci,wannan ya rage wakilcin sabuwar gwamnati,rukunin Iyad Allawi zai zama jam'iyyar hamayya mafi girma,wannan zai jawo mugun tasiri ga sabuwar gwamnatin Al-Jafari yayin da take tafiyar da harkokin mulki.(Ali)