
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 26 ga watan nan Shugaba Lien Chan na Jam'iyyar KMT ta kasar Sin da 'yan kungiyarsa sun isa birnin Nanjing na babban yankin kasar daga Taiwan ta hanyar Hongkong don yin ziyara cikin kwanaki 8 .

Mr. Lien ya kawo ziyara ne a babban yankin bisa gayyatar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da babban sakatare Hu Jintao na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suka yi masa . Kafin shekaru fiye da 50 , Jam'iyyar KMT ta ci hasara a cikin yakin basasa kuma ta yanye jiki daga babban yankin zuwa Taiwan . Ziyarar da Mr. Lien yake yi a wannan karo ta sa Mr. Lien ya zama shugaba na farko na Jam'iyyar KMT a cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce . ( Ado)
|