|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-26 17:39:20
|
Mutanen Taiwan suna mai da hankali sosai ga ziyarar da Lien Chan ke yi a nan babban yankin kasar Sin
cri
A ran 26 ga wata kafofin watsa labaru na Taiwan bi da bi ne suka bayar da labari sosai game da ziyarar da shugaban jam'iyyar Kuomingtang ta kasar Sin Mr. Lien Chan ke fara yi a babban yankin kasar Sin. Wadannan kafofin watsa labaru na Taiwan sun ce, mutanen Taiwan suna mai da hankali sosai kan ziyarar da Lien Chan ke yi a babban yankin kasar Sin.
Bisa gayyatar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da babban sakatare Hu Jintao na kwamitin suka yi masa ne, Mr. Lien Chan ya jagoranci wata kungiyar wakilan jam'iyyar Kuomingtang ta kasar Sin ya fara kawo ziyara a nan babban yankin kasar Sin a ran 26 ga watan nan. A wannan rana da yamma ne Mr. Lien Chan da 'yan rakiyarsa sun riga sun isa birnin Nanjing, babban birnin lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin domin fara ziyarar kwanaki 8 a nan babban yankin kasar Sin. (Sanusi Chen)
|
|
|