 Ran 26 ga wata da maraice Mr. Lien Chan shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya sauko babban yankin kasar Sin, don soma ziyararsa cikin kwanaki 8 . Bisa shirin da aka tsara, wani muhimmin abun da ke cikin ziyarar Lien Chan shi ne yin shawarwari da Hu Jintao babban sakatare na kwamitin tsakiya na J K S, wanda ya zama karo na farko ne babban shugaban Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da na jam'iyyar Kuomintang sun yi shawarwari tun bayan jam'iyyar Kuomintang ta kwashi hasara cikin yakin basasa a shekarar 1949, har ta tsunguna cikin tsibirin Taiwan, kuma ta yi nukura da babban yankin kasar Sin. Manazartan batun Taiwan na babban yankin kasar Sin sun nuna cewa, tattaunawar da ke tsakanin matsayin koli na jam'iyyun siyasa na gabobin biyu za ta amfanawa kara yin musanye-musanya da fahimtar juna tsakanin gabobi biyu, da ke da amfani wajen sa kaimi kan samun bunkasuwar huldar da ke tsakanin gabobi biyu.
Kafin shekaru 56 da suka shige, jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta ga bayan jam'iyyar Kuomintang cikin yakin basasa, sai jam'iyyar Kuomintang ta koma ta tsunguna tsibirin Taiwan na kasar Sin da ke da fadin muraba'in kilomita dubu 30, inda ta yi nukura da babban yankin kasar Sin. Cikin shekaru sama da 10 da suka shige, an sami ci gaba tsakanin gabobi biyu kan tattalin arziki da musanye-musanye na al'adu da ma'amalar mutane, amma ba a sa ayar yin nukura da juna ba. Kuma kafin shekaru 5 jam'iyyar Kuomintang ta rasa ikon siyasa na Taiwan, jam'iyyar kara ci gaba da demokuradiya ta kama karagar mulki, haka ya kara abubuwa masu yamutse ga makomar samun dinkuwar daya ga Taiwan da babban yankin kasar Sin. A halin yanzu cikin fasalin siyasa na Taiwan, jam'iyyar kara ci gaba da demokuradiyya ke kama karagar mulki, amma babbar jam'iyyar Kuomintang mai yin adawa ta kulla kawance tare da sauran jam'iyyu masu abota, wadanda kuma ke dauki kujeru da yawa cikin majalisar kafa dokokin shari'a, sun zama karfin siyasa mafi muhimminci cikin tsibirin.
Cikin 'yan shekarun baya, kullum bangaren babban yankin kasar Sin ta tsaya kan tabbatar da dinkuwar gabobi biyu cikin lumana ta hanyar tattaunawa, kuma an yi kokari sosai Amma hukumar Taiwan wadda jam'iyyar kara ci gaba da demokuradiya ke zama madugunta ta tafiyar da aikace-aikacen neman kawo ballewar Taiwan daga babban yankin kasar Sin, haka ya haddasa halin da ke tsakanin gabobi biyu ya tsananta. A gaban halin nan a lokaci na kafin wata guda, Hu Jintao babban sakataren JKS kuma shugaban kasar Sin ya gabatar da ra'ayinsa mai ka'idoji 4 game da bunkasa huldar da ke tsakanin gabobi biyu, babban abun da ke cikin ra'ayin shi ne bangaren babban yankin ba zai yar da kokarinsa wajen neman samun dinkuwa daya cikin lumana ba, muddin abubuwan da ke amfanawa yin musanye-musanye ga gabobi biyu kuma ga samun dinkuwa daya cikin lumana, to, bangaren babban yankin zai yi iyakacin kokarinta. A kwanaki na ba da dadewa ba, babban sakatare Hu Jintao na JKS ya gayyaci Lien Chan shugaban jam'iyyar Kuomintang da ya kawo ziyara a babban yankin.
A lokaci na kafin wata guda, Jiang Binkun mataimakin shugaban jam'iyyar Kuomintang ya shugabaci wata tawaga don kawo ziyara a babban yankin bisa gayyatar da aka yi masa, wadda ta zama share fage ne wajen yin tattaunawa tsakanin manyan shugabannin jam'iyyun biyu, har an sami ra'ayi daya na fannoni 12 kan musaye-musaye da hadin kai wajen sa kaimi ga tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarori biyu.(ASB)

|