Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-26 09:07:22    
Dalilin matsalar Taiwan na kasar Sin

cri

A ran 26 ga wata,Shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ya ja ragamar wata kungiya zuwa babban yankin kasar Sin domin yin ziyara ta kwanaki takwas,lokacin da zai bakunci babban yankin kasa,zai yi shawarwari da sakatare-janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Hu Jintao.Wannan karo ne na farko da manyan shugabanni na jam'iyyun siyasan nan biyu za su yi shawarwari tun da jam'iyyar Kuomintang ta tsugunar da kanta a Taiwan a shekara ta 1949,shi ya sa mutane na gida da na waje suke mayar da hankulansu ga matsalar Taiwan.A yau za mu yi muku bayani kan yadda aka samu matsalar Taiwan na kasar Sin da matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan warware matsalar Taiwan.

An sami matsalar Taiwan ne a shekara ta 1949.Matsalar nan ta taso ne a lokacin yakin duniya na biyu.A cikin wancan lokaci,jam'iyyar kwaminis ta Sin da jam'iyyar Kuomintang sun hada kansu wajen yakar sojojin Japan da suka kutsa cikin kasar Sin da hari.A shekara ta 1945,bayan da aka kammala yakin duniya na biyu da yakin yin adawa da harin Japan,jam'iyyar Kuomintang wadda Jiang Kai-shek ke jagaba ta kin kafa gwamnatin hadin gwiwa da jam'iyyar kwaminis ta Sin,kuma ta tayar da yakin basasa a shekara ta 1946 domin neman hallaka jam'iyyar kwaminis ta Sin da kafa gwamnatin jam'iyya daya mai mulkin kama karya.Bayan yaki na tsawon shekaru uku,jam'iyyar kwaminis ta Sin wadda ba ta  da fiffiko a sha'anin soja amma ta samu goyon baya daga jama'a ta naushe jam'iyyar Kuomintang.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekara ta 1949,Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wadda ta samu nasara ta kafa jamhuriyar jama'ar Sin.Daga bisani ba da dadewa ba kungiyoyin jam'iyyar Kuomintang sun ja da baya daga babban yankin kasar Sin har sun tsugunar da kansu a tsibirin Taiwan dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Tun fil azal Taiwan wani kashi ne na yankin kasar Sin,da akwai zirin teku tsakanin tsibirin Taiwan da babban yankin kasar Sin,tsawon makuncin zirin teku kilomita 130 ne kawai.Bayan da jam'iyyar Kuomintang ta tsugunar da kanta a Taiwan,bisa dauren gindi na Amurka ta cigaba da yin adawa da jamhuriyar jama'ar kasar Sin,halaliyar wakiliya ta kasar Sin.Tun daga wancen lokaci haka Taiwan da babban yankin kasar Sin a rabe suke  yau da shekaru 56 ke nan.

Har zuwa yanzu niyyar gwamnatin kasar Sin ta neman warware matsalar Taiwan ba ta canja ba,duk da haka ka'idar da take bi wajen warware matsalar Taiwan ta canja cikin shekaru fiye da rabin karni.Kafin shekara ta 1979 gwamnatin kasar Sin ta sha bayyana cewa za ta yantar da Taiwan da karfin soja babu mu'amala ko kadan tsakanin bangarori biyu.Bayan shekara ta 1979 gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shawarar warware matsalar gabobi biyu ta hanyar lumana.Kan kungiyoyin da suke neman balle Taiwan daga babban yankin kasar Sin da kungiyoyin kasashen waje da suke neman yin katsalanda cikin harkokin dinkuwar kasar Sin,gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa ba ta dauki alkawarin rashin amfani da karfin soja wajen neman dinkuwar kasa ba.

Kwanakin baya shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar da shawara mai ka'idoji hudu dangane da bunkasa dangantaka dake tsakanin bangarori biyu na zirin teku na Taiwan.Watau nacewa ga bin ka'idar Sin daya ba tare da tangadawa ba,ba a dakatar da kokarin neman dinkuwar kasa cikin lumana ba,ka'idar sa fata kan mutanen Taiwan ba ta canja ba,ba a yi rangwame kan ayyukan neman jawo baraka a Taiwan ba.Shugaba Hu ya kuma ce kome da zai amfanawa 'yanuwan Taiwan da kara bunkasa mu'amala tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan da kuma taimakawa kare zaman lafiya a zirin tekun Taiwan da kuma dinkuwar kasar Sin cikin lumana gwamnatin za ta yi iyakacin kokarin yin shi,kuma tabban ne za ta yi kokarin kammala shi da kyau.wannan muhimmin alkawari ne da gwamnatin ta dauka kan dimbin 'yanuwa na Taiwan.

A gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasa?hukumar koli ce mai madafun iko a kasar Sin da aka yi a watan Maris na bana an zartas da wata dokar yin adawa da barakar kasa bisa kuri'u mafin rinjaye.Fitowar dokar nan ta kawo muhimmin amfani a yanzu da tasiri mai zurfi a tarihi wajen bunkasa dangantaka dake tsakanin bangarori biyu a zirn tekun Taiwan da ciyar da harkar neman dinkuwar kasa gaba,da yin adawa da dakile ayyukan neman balle Taiwan daga babban yankin kasa da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a bangaren zirin tekun Taiwan.

Kwanakin baya an samu alamun sassautawa a hali mai tsanani da ake ciki a zirin tekun Taiwan,alal misali 'yan kasuwa na Taiwan sun yi chatar jirgin saman fasinja a ranaikun bikin yanayin bazara,an samu cigaba wajen sayar da kayayyakin amfanin gona na Taiwan a babban yankin kasar Sin.Ba da dadewa ba mataimakin shugaban jam'iyyar Kuomintang Jiang Binkun ya ja ragamar wata kungiyar zuwa babban yankin kasa,ya kuma samu ra'ayi daya kan batutuwa 12 da ma'aikatun da lamarin ya shafa na babban yankin kasar Sin wajen kara mu'amala da hadin kai a fannonin tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan.Masu binciken al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa wannan ziyara da shugaban jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin Lien Chan ya ke yi a babban yankin kasa za ta taimakawa mu'amala da fahimtar juna tsakanin bangarori biyu da cigaban dangantaka dake tsakaninsu.Ban da wannan kuma babban yankin kasar Sin zai cigaba da daukar matakai domin kara karfin dangantaka tsakani bangarori biyu wajen tattalin arziki,haka kuma zai sa kaimi da bunkasa mu'amala da hadin kai da ake yi tsakanin bangarori biyu wajen ilmi da kimiyya da fashohi da al'adu da kiwon lafiya da wasanni da kokarin kago makoma mai haske na cigaban dangantaka dake tsakanin bangarori biyu cikin lumana.(Ali)