Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-26 08:31:40    
Mr.Lien Chan yana fatan za a shimfida zaman lafiya tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan

cri

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na Taiwan suka bayar,an ce,a ran 25 ga wata,shugaban jam`iyyar Guomindang ta kasar Sin Lien Chan wanda zai kai ziyara a babban yankin kasar Sin ya yi taron ganawa da manema labarai a birnin Taibei kafin ziyararsa,inda ya bayyana cewa,yana fatan gabobi biyu na zirin Taiwan za su sanya kokari tare domin samun wadatuwa tare cikin lumana.

Mr.Lien Chan ya ci gaba da cewa,zai yi musanyar ra`ayi tare da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,wannan al`amari yana da babbar ma`ana,zai yi iyakacin kokarinsa domin kara fahimtar juna a tsakaninsu,hakan kuma za a kafa huldar aminci a tsakanin gabobin biyu na zirin Taiwan,a karshe dai za su sami wadatuwa tare.

Mr.Lien Chan ya bayyana cewa,tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a babban yankin kasar Sin,halin da babban yankin kasar Sin ke ciki a fannin siyasa da na tattalin arziki ya sami manyan sauye-sauye,saboda haka yana fatan zai yi amfani da wannan zarafi don kara saninsa game da bunkasuwar babban yankin kasar Sin,ban da wannan kuma yana fatan zai yi musanyar ra`ayi tare da shugabannin babban yankin kasar Sin daga duk fannoni wajen moriyar jama`ar Taiwan da cudanyar tattalin arziki da al`adu a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan.(Jamila Zhou)