
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , Bisa gayyatar da Babban sakatare Hu Jintao na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi masa , shugaba Lian Zhan na Jam'iyyar KMT zai jagoranci kungiyar wakilan jam'iyyar zuwa babban yankin kasar Sin don ziyara daga ran 26 ga watan nan zuwa ran 3 ga watan Mayu .
An labarta cewa a ran 18 ga watan nan a nan birnin Beijing , Chen Yunlin , direktan Ofishin harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin da Lin Fengzheng , sakataren tsakiya na Jam'iyyar KMT ta Sin sun tattauna ajandar ziyarar Lian Zhan a babban yanki. Mr. Lian da 'yan kungiyarsa za su yi ziyara a birnin Nanjing da Beijing da Xi'an da kuma birnin Shanghai. ( Ado)
|