Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-18 14:33:37    
Hu Jintao ya nuna maraba kuma ya gayyaci Song Chuyu da ya ja ragamar kungiyar wakilan jam'iyya don kawo ziyara

cri

A ran 18 ga watan nan a nan birnin Beijing, Chen Yunlin, darektan ofishin kula aikin taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, bisa ikon da aka danka masa ya sanar da cewa, Hu Jintao, babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya nuna maraba kuma ya gayyaci Song Chuyu, shugaban jam'iyyar Qingmingdang da ya ja ragamar kungiyar wakilan jam'iyya don kawo ziyara a babban yankin.

Kwanakin baya bangaren jam'iyyar Qinmingdang ya nuna fili cewa, shugaba Song Chuyu yana fatan zai ja ragamar kungiyar wakilai don kawo ziyara a babban yanki kafin ran 14 ga watan Mayu. Chen Yunlin ya yi fatan, za a aiko mutane don yin shirye shirye, kuma ya yi imani, ziyarar da shugaba Song zai kawo za ta sa kaimi ga cudanyar da za a yi a tsakanin gabobi biyu da sassauta halin da a ke ciki a tsakanin gabobi biyu. (Dogonyaro)