|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-15 17:32:14
|
An bayyana wa jami'an soja na kasashen waje da ke nan kasar Sin "Dokar hana ballewa daga kasa"
cri
A ran 15 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ofishin harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Zhang Mingqing ya bayyana wa jami'an soja na ofisoshin jakadancin kasashen waje fiye da 40 da ke nan kasar Sin yadda kasar Sin ta tsara "Dokar hana ballewa daga kasa".
Mr. Zhang ya nuna cewa, tsara wannan doka da kasar Sin ta yi yana daidai da ra'ayin jama'ar kasar Sin, ya kuma bayyana ra'ayin bangarori daban-dabam na kasar Sin da na Sinawan ketare. Wannan doka tana da muhimmanci sosai ga kiyaye dinkuwar dukkan yankunan kasar Sin da zaman lafiya a yankin gabashin Asiya. (Sanusi Chen)
|
|
|