Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-13 14:14:55    
Babban yankin kasar Sin ba ya nuna bambanci ga jam'iyyun siyasa na Taiwan wajen yin shawarwari

cri
Kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwa ta kasar Sin Mr Li Weiyi ya bayyana ran 13 ga wata a nan birnin Beijing cewa, bangaren babban yankin kasar ya bayyana manufofinsa a fili dangane da batun yin tattaunawa a tsakaninsa da jam'iyyun siyasa na Taiwan, ba ya nuna bambanci ga ko wane mutun wajen yin shawarwari, haka nan kuma ba ya kin yin tattaunawa da wanda ke rike da hukuma ba.

Malam Li Weiyi ya yi wannan kalami ne a gun taron watsa labaru da ofishin kula da harkokin Taiwan na kasar ya shirya a wannan rana. Ya kuma kara da cewa, abin da ke jawon hankalin babban yankin shi ne manufofi da jam'iyyun siyasa na Taiwan ke aiwatarwa da ra'ayoyinsu a kan shawarwari tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan. Duk mutane da jam'iyyun siyasa, ko me suka yi ko kuma kome suka fada, idan yanzu sun amince da ra'ayi daya na ran 2 ga watan Satumba wanda ke bayyana ka'idar kasar Sin daya tak a duniya, bangaren babban yanki zai dauke su bisa matsayi iri daya, zai yi ma'amala da su. (Halilu)