Methadone wani ruwan magani da aka hada ta hanyar kimiyya,yana da amfani ga masu shan miyagun kwayoyi wajen yanke kaunarsu da shan miyagun kwayoyi.Shi ya sa a kasashe da yawa na duniya ana amfani da wannan magani wajen taimakawa masu shan miyagun kwayoyi yanke kaunarsu da shan miyagun kwayoyi.Masu shan miyagun kwayoyi za su iya kaucewa shan miyagun kwayoyi idan sun sha maganin methadone yadda ya kamata bisa shawarwarin likitoci,ta haka kuwa an dakile yaduwar cutar sida ta hanyar sa allurar miyagun kwayoyi.
Bisa labaran da aka samu,an ce kasashe da bangarori da yawa na duniya aka yi amfani da wannan maganin methadone.Wani profesa na kolejin koyon ilmin likitanci na jam'ar Beijing Mista Li Zhiwei yana mai ra'ayin cewa wani muhimmin burin da aka sa gaba wajen amfani da maganin methadone a asibiti shi ne a rage yawan miyagun kwayoyin da masu shansu ke sha ta hanyar allura da rigakafin cututtukan sida da rage su.Ya ce, "domin rigakafin cutar sida,mu kan yi kira ga kungiyoyin jama'a da su ba da wani magani maimakon miyagun kwayoyi ga masu shan miyagun kwayoyi ta yadda za su iya bar shan miyagun kwayoyi ta hanyar sa allura da kare su daga cutar sida.An yi amfani da maganin methadone ne duk domin rage lahanin da shan miyagun kwayoyi ta hanyar sa allura da aka kawo wa masu shan miyagun kwayoyi da iyalansu da kuma zamatakewar al'umma."
Asibitin birnin Gejiu a lardin Yunnan dake kudu maso yammancin kasar Sin,asibiti ne na farko da ya yi amfani da maganin methadone.Mista Ming Xiangdong,wani likita ne dake aiki a asibitin.Ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa tun da aka yi amfani da maganin methadone a wannan asibiti dag watan Afrilu na shekara ta 2004,kome na tafiya daidai. An sami mutane kimanin dari sun sha maganin nan a wannan asibitin. Ya ce masu shan miyagun kwayoyi sun fi shan magani methadone maimakon miyagun kwayoyi.A wata daya aka sami mutane sama da 80 da suka sha maganin methadone.Yawansu zai karu watakila za su kai 250 zuwa 300 bisa shirin da aka tsara.Masu shan miyagun kwayoyi da iyalansu suna jin dadi kan hanyar da ake bi a wannan asibiti wajen taimakawa masu shan miyagun kwayoyi yanke kaunarsu da shan miyagun kwayoyi.
Mista Ming Xiangdong ya kuma bayyana cewa bisa tsarin ka'idojin da gwamnatin kasar Sin ta tsara,duk wanda yawan shekarunsa ya wuce 20 da haihuwa kuma aka taba tilasta musu da su kaucewa shan miyagun kwayoyi har yanzu ba su bar wannan mugun hali na shan miyagun kwayoyi ba ya iya neman damar shan maganin methadone,duk kudin da ya kashe domin sha magani gwamnati ce ta biya masa.
Mallama Wang Yu wata mace ce da ta sha miyagun kwayoyi na tsawon shekaru fiye da 10.Ga shi a yau tana da shekaru 34 da haihuwa.Da aka fara samar maganin methadone a asibitin birnin Gejiu,ita ce tana daya daga cikin wadanda suka fara shan maganin nan a asibitin.Kusan kowace rana da karfe hudu na yamma ta zo asibitin ta sha magani.Yanzu ta bar shan miyagun kwayoyi,ta yi zama kamar yadda sauran mutane suke.Ta gaya wa wakilinmu cewa Bayan da na sha maganin methadone, na ji karfi.ban gaji ba kamar yadda na yi a da da kuma babu abin da na sha'awa,ga shi a yau mutane da yawa sun ce ina da koshin lafiya,ni ma ina jin haka.
Tun farkon watan Afrilu na shekara ta 2004,gwamnatin kasar Sin ta amince da lardin Yunnan da Guangdong da sauran larduna uku su yi amfani da maganin methadone.Da akwai asibitoci guda 8 a kasar Sin da suka samar da maganin methadone ga masu shan miyagun kwayoyi.(Ali)
|