A ran 7 ga watan nan , Kwamitin shugabanni wanda yana kunshe da Jalal Talabani , sabon shugaban kasar Iraq da Abdul Mahdi da Ghazi Yawal , mataimakan shugaban ya yi rantsuwar hau mukami a birnin Bagadaza . Sa'an nan kuma kwamitin din nan ya na da Ibrahim Jafari , shugaban Jam'iyyar hadin gwiwar Iraq da ya zama firayin ministan rikon kwarya mai cikakken iko , kuma shi ne zai kafa Majalisar ministoci . Ta haka mutanen Iraq sun fara kula da kasar Iraq .
Bisa labarin da aka bayar , an ce , a cikin makonni biyu masu zuwa , Malam Jafari zai kammala aikin kafa majalisar ministoci . Zai gabatar da sunayen ministoci ga Majalisar wucin gadi don jefa kuri'u . In sun sami goyon bayan 'yan majalisa na kashi 50 cikin 100 , sai za a zartas da su .
Hajim Hassani , shugaban majalisar wucin gadi ta kasar Iraq
A ran 7 ga watan nan ya bayyana cewa , Malam Alawi , firayin ministan rikon kwarya ya riga ya mika takardar yin murabus , amma har ila yau yana ci gaba da aikin majalisar ministoci ta wucin gadi har zuwa lokacin kafuwar sabuwar majalisar ministoci.
Bisa shirin da aka yi , an ce . Ya kamata a ran 15 ga watan Agusta na wannan shekara a tsara tsarin mulkin kasar Iraq . Amma saboda yanzu rukunoni daban daban suna kasancewa da sabani kan matsalar tsara tsarin mulkin kasar , shi ya sa za a samun bambancin ra'ayoyi , kuma mai yiwuwa ne za a kauce wa kwarya-kwaryar yarjejeniyar da jam'iyyun majalisar suka daddale. Kuma sun yi fatan Jalal Talabanni , shugaban Jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Kurdawa da Ibrahim Jafari, shugaban Jam'iyyar United Iraqi Alliance su musanya ra'ayoyinsu kan matsalar tsara tsarin mulkin kasar .
Ko da ya ke shugaban majalisar ba zai kawo tasiri mai yawa a cikin zaman siyasa na nan gaba ba , amma duk da haka ko ya iya shawo kan 'yan majalisar da su kawar da bambancin ra'ayoyi kan tsarin mulkin kasar . Kuma shugaban majalisar zai kula da aikin rarraba mukamin cikin majalisar, saboda haka wannan batu ya zama muhimmin abu na gwagwarmayar
tsakanin rukunoni daban daban .
Jama'ar kasar Iraq suna son za a sa aya kan mamayewar kasashen waje kuma tabbatar da mulkin kai . Yanzu a kasar ba a bar sojojin kasar Amurka ba a wajen kiyaye odar kasar Iraq . Wannan kuma babbar matsala ce a gaban Malam Jafari.
Sa'an nan kuma Mr. Jafari yana fuskantar wasu matsalolin diplomasiya .
Masu binciken al'amuran duniya sun yi nuni da cewa , idan Malam Jafari yake son tabbatar da aikin tsara tsarin mulkin kasa da shirya aikin jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a da shirya babban zabe, to , zai dauki nauyin dake wuyansa . Ma iya cewa, tabbas ne a cikin gudanarwar farfado da siyasar kasar Iraq Malam Jafari zai sha wahaloli masu yawa , sai mu jira mu gani . (Ado)
|