Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-05 14:24:22    
An zarki 'dan kawo baraka na Taiwan da su kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni

cri
A ran 4 ga wata, Su Jinqiang, shugaban kungiyan 'yan kawo baraka ta Taiwan wato "kawancen hadin kan Taiwan" ya shugabanci wata kungiyar zuwa Japan don kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni, sabo da haka ya sha suka mai zafi daga wajen sassan siyasa na Taiwan.

Jaridar "People's Daily" da aka buga a ran 5 ga wata a babban yankin kasar Sin ta tsamo maganar Zhang Rungong, kakakin jam'iyyar KMT ta kasar Sin, daya daga cikin muhimman jam'iyyun siyasa na Taiwan cewa, Su Jinqiang ya kai ziyarar ban girma ga makabartar Yasukuni bisa matsayinsa na shugaban jam'iyyar siyasa ta Taiwan, wannan ya bayyana cewa, "kawancen hadin kan Taiwan" yana nuna girmamawa ga sojancin Japan, idan rukunin 'yan kawo baraka na Taiwan suna son hadin gwiwa da 'yan ra'ayin mazan jiya na Japan domin yin gaba da babban yankin kasar Sin, to wannan danyen aiki ba shi da amfani ga Taiwan ko kusa. (Umaru)