|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-01 17:36:44
|
Ana fata za a kara yin kokari wajen shimfida zaman lafiya a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan
cri
A ran 1 ga wata, kungiyar da ta kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ta jam'iyyar Kuomingtang ta kasar Sin wadda ke karkashin mataimakin shugaban jam'iyyar Chiang Pin-kung ta gama ziyararta a nan babban yanki lami lafiya kuma ta tashi daga nan birnin Beijing zuwa Taiwan. Kafin ya tashi, Mr. Chiang Pin-kung ya bayyana cewa, yana farin ciki sosai domin ya kafa wata gada domin shimfida zaman lafiya a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Mr. Chiang ya kuma yi fata a nan gaba mutane masu da yawa za su ketare wannan gada su kara yin kokari wajen shimfida zaman lafiya a tsakanin mashigin tekun Taiwan.
Chiang Pin-kung ya kuma ce, a nan gaba idan shugaban jam'iyyar Kuomingtang ta kasar Sin Lian Zhan ya kawo wa babban yankin ziyara, zai kuma ingiza shimfida zaman lafiya a gabobi 2 na mashigin Taiwan. (Sanusi Chen)
|
|
|