A ran 30 ga watan jiya da dare,kungiyar wakilan jam`iyyar KMT wato Guomindang ta kasar Sin wadda ta zo babban yankin kasar Sin daga lardin Taiwan na kasar Sin ta yi shawarwari da ofishin aikin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da sassan da abin ya shafa kan batu game da yadda za a bunkasa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan.
Wakilan `yan kasuwa na Taiwan dake nan birnin Beijing sun yi maraba ga wannan kuma sun bayyana cewa,suna fatan jam`iyyar KMT ta kasar Sin za ta yi hakikanan ayyuka don bunkasa cudanya a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan.
A ran 31 ga watan jiya,shugaban kungiyar kamfanonin jarin Taiwan na birnin Beijing Xie Kunzong ya bayyana cewa,idan ana so a kafa wani muhalli mai zaman lafiya da zaman karko a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan,to,dole ne a sa kaimi ga cudanya tsakaninsu.(Jamila zhou)
|