A ran 31 ga watan jiya a nan birnin Beijing,direktan ofishin aikin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin Chen Yunlin ya bayyana cewa,muddin dai jam`iyyar Minjin ta Taiwan ta bar da tsarin jam`iyyarta na neman `yancin kan Taiwan kuma ta daina yin aikin neman `yancin kan Taiwan,to,babban yankin kasar Sin zai yi cudanya da ita.
Mr.Chen Yunlin ya fadi hake ne yayin da yake amsa tambayoyin da menama labarai suka yi masa.Ya ce,babban yankin kasar Sin ya yi maraba ga `ra`ayi daya da aka samu a shekara ta 1992` kuma ya nuna kiyayya ga makarkashiyar `yancin kan Taiwan.Muna so mu yi shawarwari da dukkan mutane ko jam`iyyu wadanda ke yin na`am da ka`idar kasar Sin daya tak a duniya da `ra`ayin daya da aka samu a shekara ta 1992`.(Jamila Zhou)
|