 Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, Ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Taro na 2 na Majalisar wucin gadi ta kasar Iraq bai sami sakamako ba .
A ran 29 ga watan nan , Majalisar wucin gadi ta kasar Iraq ta yi taro na biyu . Amma taron bai zabo shugaban majalisar cikin lokaci ba, kuma bai yi shiri kan kafuwar sabuwar gwamnati ba .
Bisa shirin da aka yi , an ce . Ya kamata a wannan taron a zabi shugaba 1 da mataimakan shugabanni 2 . Saboda Ghazi Yawar , shugaban rikon kwarya na kasar Iraq kuma shugaban 'yan darikar Sunni ya ki karbar mukamin shugaban majalisar da aka gabatar , shi ya sa a karshe dai taron ya tsai da kudurin jinkirtad da lokacin zaben shugaban majalisar . Bisa labarin da aka bayar , an ce , a ran 3 ga watan Afrilu majalisar wucin gadi za ta sake yin taro , ta yadda za a tsai da sunayen shugaban majalisar da mataimakan shugabanninta .
Ko da ya ke majalisar wucin gadi ta kasar Iraq ta yi taruruka biyu , amma ba ta zabi shugaban majalisar ba . Wannan ya sa an kasa gudanar da farfadowar siyasar kasar Iraq har sau biyu . Babban dalilin da ya sa aka yi haka shi ne yanzu rukunoni daban daban suna kasancewa da sabani kan matsalar rarraba mukami. Ban da ministan kudi da ministan man fetur , jam'iyyun majalisar sun riga sun daddale kwarya-kwaryar yarjejeniya. Kuma sun yi fatan Jalal Talabanni , shugaban Jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Kurd zai zama shugaban kasar, kuma Ibrahim Jafari, shugaban Jam'iyyar United Iraqi Alliance zai zama firayin minista . Sa'an nan kuma wani 'dan addinin Sunny zai zama shugaban majalisar .
Saboda ya kasance da wadannan sabani , shi ya sa a lokacin taro na biyu na majalisar wucin gadi an yi cacar baki ba tare da tsayawa ba . Mr. Yawar ya bar wurin taron kafin lokacin rufe taron . 'yan majalisar masu yawa sun yi bakin ciki saboda an sake jinkirtar da lokacin zaben shugaban majalisar , kuma sun nemi a jefa kuri'a a ran nan . Bugu da kari kuma sun kushe jam'iyyar United Iraqi Alliance da jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Kurdawa da cewa, sun yi magudi kan batun kafa majalisar ministoci kuma sun nemi shugabannin wadanan jam'iyyu da su sanar da cikakkun abubuwa kan shawarwarin tsakanin bangarorin biyu ga majalisar da jama'ar kasar Iraq .
Ko da ya ke shugaban majalisar ba zai kawo tasiri mai yawa a cikin zaman siyasa na nan gaba ba , amma duk da haka tsai da sunan shugaban majalisar zai shafe tsarin rarraba mukamin , saboda haka wannan batu ya zama muhimmin abu na gwagwarmayar tsakanin rukunoni daban daban . Bayan da aka zabi shugaban majalisar , majalisar wucin gadi za ta zabi shugaban kasar da mataimakin shugaban kasar. Sa'an nan kuma kwamitin shugabanni zai gabatar da sunan firayin minista da mambobin majalisar ministoci , kuma za a tsara tsarin mulkin kasar .
Masu binciken al'amuran duniya sun kiyasta cewa , daga wahalolin da aka haddasa a cikin zaben shugaban majalisar , ma iya cewa, tabbas ne gudanarwar farfado da siyasar kasar Iraq za ta gamu da matsaloli, sai mu jira mu gani . (Ado)
|