A ran 29 ga watan nan a birnin Beijing Zhu Peikang , mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na kwamitin juyin juya hali na Jam'iyyar KMT ta Kasar Sin ya gana da manema labaru , inda ya nuna maraba ga kungiyar da ke ziyara a babban yanki ta jam'iyyar KMT wadda Chiang Pin-kun , mataimakin shugaban Jam'iyyar ke jagoranci .
Mr. Zhu ya ce , Mr. Chiang ya shugabanci kungiyar wakilai don kawo ziyara a babban yaki a wannan karo, hakan ya dace da moriyar jama'ar gabobi biyu na Zirin Taiwan , kuma yana da babban amfani a wajen sa kaimi kan musanye-musanye da hadin kai na tsakanin gabobi biyu .Ya yi fatan Kungiyar za ta mika fatan alheri daga farar hula na babban yanki ga 'yan uwan Taiwan . ( Ado)
|