Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-31 17:19:48    
Babban yankin kasar Sin yana mai da muhimminci kan sa kaimi ga yin musanye-musanye da hadin kai na tattalin arziki da ciniki tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan

cri
Ran 31 ga wata a birnin Beijing, Tang Jiaxuan dan majalisar harkokin kasar Sin ya gana da tawagar jam'iyyar Kuomintang wadda ke karkashin jagorancin Jiang Binkun mataimakin shugaban jam'iyya. Ya nuna cewa, babban yankin kasar Sin yana mai da muhimmanci kan musaye-musaye da hadin kai na bangarorin tattalin arziki da ciniki tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, kuma za a bayar da manufofi da matakai masu gatanci.

Tang Jiaxuan ya ce, babban yankin Sin yana son yin musanya ra'ayoyi tare da duk jam'yyun siyasa da kungiyoyi da mutane na Taiwan wadanda ke yin adawa da 'yan samun yancin kai da tsayawa kan bunkasa dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu, kan batutuwan da ke jawo hankulan 'yan uwa na gabobi biyu, don sa kaimi tare kan kyautata da bunkasa huldar nan.(ASB)