Ran 30 ga wata, a birnin Beijing, Tang Jiaxuan, dan majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gana da Shayam Saran, sakataren harkokin waje na kasar India, wanda ya zo kasar Sin ne domin halarci taro na karo na 15 na kungiyar hadin gwiwa mai kula da aikin tabbatar da iyakar bodar da ke tsakanin kasar Sin da kasar India. A gun ganawa da aka yi, Mista Tang ya yi nuni da cewa, yana fata bangarorin 2 za su dauki sahihan matakai domin ciyar da dangantakar aminci da hadin gwiwa mai amfani da ke tsakaninsu gaba zuwa wani sabon matsayi.
Ban da wannan kuma, Mista Tang ya nuna yabo ga kungiyar tabbatar da iyakar bodar. Ya yi imani cewa, muddin bangarorin 2 su tsaya kan manufar yin shawarwarin daidai wa daida da yin hakuri ga juna, za su samu turba mai adalci da dukan bangarorin 2 za su yarda da ita domin daidaita maganar iyakar bodar.
Mista Saran ya nuna cewa, gwamnatin kasar India da jama'arta suna zura ido kan ziyarar da Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin zai kai wa kasar India. Kuma yana tattare da imanin cewar ziyarar Mista Wen za ta haifar da sakamako mai kyau, da kuma ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen 2 gaba. (Bello)
|