Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-31 10:15:05    
Direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na JKS ya gana da kungiyar kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ta Jam'iyyar KMT

cri
Wakilin rediyo kasar Sin ya ruwaito man labari cewa, A daren ran 30 ga wannan wata, a na birnin Beijing, direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mr Chen Yunlin ya gana da kungiyar kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara ta jam'iyyar KMT da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban Jam'iyyar KMT, bangarorin biyu sun yi shawarwari kan batun kara inganta hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya da na sa kaimi ga samun bunkasuwa gaba dayansu da dai sauran batutuwa.

Mr Chen Yunlin ya ce, ziyarar da kungiyar JGD ta kawo wa babban yankin kasar Sin ta soma shawarwarin da ke tsakanin jam'iyyun biyu, wannan ya bayyana burin 'yanuwan bangarorin biyu na fatan samun bunkasuwa da wadatuwa gaba daya. Ya ce, babban yankin kasar Sin yana son amincewa da ra'ayi daya da aka samu a shekarar 1992 da kuma yin adawa da neman 'yancin Taiwan, da yin tsayawa tsayin daka ga yin shawarwari da ma'amala da jam'iyyu daban daban da rukunoni daban daban da mutanen musamman na Taiwan wadanda suke son raya huldar da ke tsakanin bangarorin biyu don sa kaimi ga samun bunkasuwa sannu a hankali kuma lami lafiya cikin hadin guiwa.

Mr Jiang Bingkun ya nuna godiya ga bangaren babban yankin kasar Sin saboda ya yi musu karbansu da aka yi cikin halin aminci sosai. Ya ce, yin ma'amala a tsakanin bangarorin biyu na da taimako ga sassauta hali mai zafi a Zirin Taiwan , kuma na da amfani ga yin hadin guiwar gaggauta samun bunkasuwa a tsakanin bangarorin biyu da na da amfani ga jama'ar bangarorin biyu, saboda haka ya kamata bangarorin biyu su sa kaimi ga ma'amalar tsakanin bangarorin biyu bisa hakikanin abubuwa.(Halima)