Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-31 10:13:14    
JKS da KMT sun sami ra'ayi daya ga yin ma'amala da hadin guiwa wajen tattalin arziki da cinikayya

cri
Wakilin Rediyo kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa, direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na kwamitin Tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Mr Chen Yun Lin da wakilan sassan da abin ya shafa da kungiyar masu kawo ziyara a babban yankin kasar Sin ta Jam'iyyar KMT da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam'iyyar KMT Mr Jiang Bingkun sun yi shawarwari a tsakaninsu kuma sun sami ra'ayi daya a kan sa kaimi ga yin mu'amala da hadin guiwa da ke tsakanin bangarorin biyu na Zirin Taiwan a ran 30 ga watan Maris a nan birnin Beijing.

Mr Chen Yun Lin da Mr Jiang Bingkun dukansu sun bayyana cewa, yin yunkurin sa kaimi ga yin ma'amala da hadin guiwa wajen tattalin arziki a tsakanin bangarorin biyu na da amfani ga kara dankon huldar tattalin arziki da ke tsakanin bangarorin biyu da kuma sasaauta hali mai tsanani da ake ciki a tsakanin bangarorin biyu, sa'anan kuma na da amfani ga kara daga karfin takara na Taiwan wajen tattalin arziki, wannan ya dace da moriya daya na 'yanuwan da ke tsakanin bangarorin biyu.

Bayan shawarwarin da suka yi, bangarorin biyu sun tsai da kuduri na sa kaimi ga harkokin yin kwangilar zirga-zirgar jiragen sama don yin sufurin fashinjoji da kayayyaki da kuma ci gaba da samar da sauki ga 'yanuwan bangarorin biyu wajen kai da kawowa a tsakaninsu, da kuma kara inganta hadin guiwa wajen noma, da daidaita batun sayar da amfanin gona na Taiwan a babban yankin kasar Sin da ciyar da harkokin kudi da na inshora da ke tsakanin bangarorin biyu gaba, a nace ga kiyaye fa'idar da 'yanuwan Taiwan suka samu yadda ya kamata wajen zuba jari a babban yankin kasar Sin bisa dokokin shari'a, da sa kaimi ga yin ma'amalar a tsakanin sassan birane da gundumomi da garuruka na bangarorin biyu da kuma sa kaimi ga yin ma'amalar watsa labaru da ba da ilmi a tsakaninsu , kuma cikin himma da kwazo ne za a yi shirin yawon shakatawa da mazaunan babban yankin kasar Sin za su iya yi a Taiwan da kuma sa kaimi ga yaki da laifufuka cikin hadin guiwa a tsakaninsu.(Halima)