Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-30 21:13:41    
Kungiyar wakilan jam'iyyar Koumingtang ta kasar Sin ta iso nan birnin Beijing

cri

A ran 30 ga wata da yamma, kungiyar wakilan jam'iyyar Koumingtang ta kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin mataimakin shugabanta Chiang Pinkun ta iso nan birnin Beijing daga birnin Nanjing na lardin Jiangsu domin ci gaba da yin ziyararta a nan babban yankin kasar Sin.

A filin jirgin sama na Beijing, Mr. Chiang Pinkun ya gaya wa manema labaru cewa, yana fata ziyarar za ta ba da amfani ga ingiza musanye-musanyen tattalin arziki da cinikayya a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da kuma sassauta hali mai tsanani da ake ciki a tsakanin Taiwan da babban yankin.

Bisa shirin da aka shirya, shugaban ofishi mai kula da harkokin Taiwan na kasar Sin Chen Yunlin zai shirya liyafa don Chiang Pinkun da 'yan rakiyarsa.

A ran 28 ga wata da yamma ne Chiang Pinkun da 'yan rakiyarsa suka iso babban yankin kasar Sin sun fara yin ziyarar kwanaki 5 a babban yankin. (Sanusi Chen)