
A ran 29 ga wata da yamma,kungiyar wakilan jam`iyyar Guomindang ta kasar Sin wadda ke karkashin shugabancin Mr.Jiang Bingkun,mataimakin shugaban jam`iyyar Guomindang ta kasar Sin ta isa birnin Nanjing na lardin Jiangsu daga birnin Guangzhou na lardin Guangdong cikin jirign sama,za ta ci gaba da yin ziyara a babban yankin kasar Sin.
A ran 29 ga wata da dare,sakataren kwamitin lardin Jiangsu na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma direktan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama`ar lardin Jiangsu Li Yuanchao ya yi ganawa da Mr.Jiang bingkun da `yan rakiyarsa kuma ya kira liyafa domin su.Mr.Li Yuanchao ya bayyana cewa,kamata ya yi mu sinawa mu ciyar da babban sha`anin dayantakar kasa da wadatuwar kasa gaba.
Mr.Jiang Bingkun ya bayyana cewa,`yan kasuwa da suka zo wurin daga Taiwan suna da yawa,kamata ya yi a kara cudanyar tattalin arziki da ciniki a tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan ta yadda za a daga matsayin zaman rayuwar jama`ar gabobi biyu na zirin Taiwan tare.
A ran 30 ga wata da yamma,Mr.Jiang Bingkun da `yan rakiyarsa za su tashi daga birnin Nanjina kuma za su zo nan birnin Beijing domin ci gaba da ziyararsu.(Jamila zhou)
|