
A ran 28 ga wata da safe, Chiang Pin-kun, mataimakin shugaban jam'iyyar Koumintang ta Taiwan ya shugabanci wata kungiyar wakilai 34 zuwa birnin Guangzhou na babban yankin kasar Sin domin yin ziyarar kwananki 5 a babban yankin. Wannan ne karo na farko da jam'iyyar KMT ta kafa kungiyar wakilanta domin kawo wa babban yankin kasar Sin ziyara bayan ta je tsibirin Taiwan a shekarar 1949.

Kafin ya tashi daga Taiwan, Chiang Pin-kun ya ce, loakcin da suke yin ziyara a babban yankin kasar Sin, za su tuna da Sun Yat-sen a birnin Nanjing. Ban da wannan, kungiyar da hukumomin da abin ya shafa na babban yanki za su tattauna ko za su yi musayar ra'ayoyi kan wasu matsalolin ciniki da na tattalin arziki da ke kasancewa a tsakanin Taiwan da babban yankin. (Sanusi Chen)
|