A cikin kwanakin nan, kasashen duniya suna ci gaba da goyon bayan "dokar hana ballewa daga kasa" da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas.
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Zimbabuwei ta bayar da sanarwa a ran 24 ga watan nan cewa, kasar Zimbabuwei tana tsayawa tsayin daka kan kasar Sin daya tak, kuma "dokar hana ballewa daga kasa" ta share fage domin tabbatar da samun zaman lafiya da kuma dinkuwar kasar Sin.
Haka kuma shugaban kasar Libya Muammar al-Qadhafi ya yi bayani a ran 23 ga watan nan cewa, kasar Libya tana goyon bayan manufar kasar Sin daya tak, da kuma dukkan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka domin kiyaye mulkin kai da cikakken yankunan kasar Sin, kuma ta ki yarda da a balle yankin Taiwan daga kasar Sin.
Ban da wannan kuma, kasashen Lebanon da Sudan da Cote d'Ivoire da kuma Moldova sun nuna goyon baya ga kasar Sin kan matsayinta wajen batun Taiwa ta hanyoyi daban daban a cikin kwanakin nan.(Kande Gao)
|